Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ɗage sauraron shari’ar tsohon Antoni-Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami, zuwa ranar 7 ga Janairu, domin yanke hukunci kan bukatar belin da ya gabatar.
Abubakar Malami na fuskantar tuhume-tuhume na safarar kuɗi da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta shigar a kansa. A halin yanzu, ana tsare da shi a gidan gyaran hali na Kuje tare da ɗansa, Abdulaziz Malami, da ɗaya daga cikin matansa, Bashir Asabe, waɗanda suma ake tuhuma a gaban kotun.
EFCC ta gurfanar da su ne bisa tuhume-tuhume guda 16, tana zarginsu da safarar kuɗaɗe da yawansu ya kai Naira biliyan 8.7.
Lokacin da aka karanto musu tuhume-tuhumen a ranar 29 ga Disambar 2025, dukkan waɗanda ake tuhumar sun musanta zargin da ake yi musu.
Kotun ta ce za ta bayyana matsayinta kan bukatar belin a ranar da aka sanya, yayin da ake ci gaba da tsare su har zuwa lokacin yanke hukuncin.
