HomeLabarai‎Gwamnatin Plateau Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane 4 Kan Cutar Lassa ...

‎Gwamnatin Plateau Ta Tabbatar da Mutuwar Mutane 4 Kan Cutar Lassa ‎

-

‎Gwamnatin Jihar Plateau ta tabbatar da mutuwar mutane huɗu sakamakon kamuwa da cutar Lassa a jihar.

‎Tabbacin hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Plateau ta fitar, inda ta ce an samu mutuwar mutanen ne bayan an tabbatar sun kamu da cutar ta hanyar gwaje-gwajen asibiti.

‎Sanarwar ta bayyana cewa gwamnati ta ɗauki matakan gaggawa domin dakile yaɗuwar cutar, ciki har da ƙarfafa sa ido a cibiyoyin lafiya, wayar da kan jama’a, da kuma ba da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya.

‎Ma’aikatar ta kuma shawarci al’umma da su ƙara kula da tsaftar muhalli, su guji hulɗa da beraye da duk wani nau’in abu da ke alaƙa da cututtuka, tare da hanzarta zuwa asibiti idan aka fara jin alamomin cutar.

‎Gwamnatin jihar ta ce za ta ci gaba da sanar da jama’a duk wani sabon bayani da ya shafi ci gaban lamarin yayin da take ƙara ƙaimi wajen hana yaɗuwar cutar Lassar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

ADC Ta Zargi Tinubu Da Raba Kan ‘Yan Adawa Ta Hanyar NDC

Jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC na da hannu wajen ƙirƙirar sabuwar jam’iyyar NDC domin raunata haɗin...

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates to Madrid Chiefs

Vinicius Jr Accused of Reporting Teammates’ Issues to Real Madrid Chiefs. Reports from several European media outlets claim that Vinícius Júnior is being accused of informing...

Most Popular