Babbar Kotun Jihar Sokoto ta yanke wa mutum uku hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan samunsu da laifukan da suka shafi ta’addanci da yaɗa makamai ba bisa ka’ida ba.
Kamar yadda Majiyarmu ta TRT Hausa ta ruwaito ta ce, Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da Yusuf Muhammad (wanda aka fi sani da Sallau), ɗan ƙasar Nijar; Jabbi Alhaji Yalle; da Kabiru Muhammad.
Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ta kama su ne a ranar 13 ga Yunin 2025 ta hannun sashenta na yaƙi da ta’addanci, bisa zarginsu da hannu a ayyukan safarar makamai da ta’addanci da suka shafi ƙetare iyakoki.
An saurari shari’ar mai lamba SS/45c/2026 a gaban Mai Shari’a Muhammad Nuraddeen Bello na Kotun Jihar Sokoto mai lamba 23.
Yayin da yake yanke hukunci, Mai Shari’a Bello ya samu mutanen ukun da laifukan da ake tuhumarsu da su, tare da yanke musu hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Kotun ta kuma bayar da umarnin kwace duk kuɗaɗen da aka samu a hannunsu tare da miƙa su ga Gwamnatin Tarayya.
Mai Shari’a Bello ya ce: “Wannan hukunci shi ne sabuwar nasara a jerin shari’o’in da DSS ta samu nasarar gurfanarwa, a ci gaba da ayyukanta na yaƙi da ta’addanci da ƙungiyoyin aikata manyan laifuka da ke aiki ta hanyar ƙetare iyakokin Nijeriya.”
