Akalla mutane huɗu ne suka mutu, yayin da wasu 14 ke kwance a asibitoci bayan sun sha wani maganin gargajiya da ake zargin yana ɗauke da guba a garin Oju da ke Jihar Benue.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Lamarin ya faru ne a yankin al’ummar Igede, bayan wasu mazauna garin sun sayi tare da shan maganin a kasuwar Ihiejwo a ƙarshen makon da ya gabata.
Rahotanni sun bayyana cewa ana zargin wasu mutane uku da suka hada da Magani, Mohamed da Kala ne suka sayar da maganin ga mazauna yankin.
An fara samun labarin lamarin ne a ranar 2 ga Nuwamba, 2026, bayan mutanen da suka sha maganin suka fara fama da matsalolin lafiya iri ɗaya.
Bayanai sun nuna cewa mutum na farko ya mutu a safiyar Talata, yayin da wani ya rasu da sanyin safiyar Laraba. Haka kuma, wasu mutum biyu sun mutu a ranar 4 ga Nuwamba.
Bayan faruwar lamarin, matasan ƙungiyar Igede Youth Council tare da shugabancin matasan ƙaramar hukumar Oju sun cafke mutanen uku da ake zargi da sayar da maganin, inda suka miƙa su ga rundunar ’yan sanda.
Shugaban ƙungiyar matasan Igede, John-Frank Ozzidi, ya buƙaci gwamnatin jihar ta gudanar da cikakken bincike tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu a lamarin.
Ya ce matasan sun guji ɗaukar doka a hannunsu ne saboda amincewarsu da hukumomin gwamnati wajen tabbatar da adalci.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Oju, Jackson Ominyi, ya tabbatar da faruwar lamarin, amma ya ce har yanzu bai tabbatar da ainihin adadin mutanen da suka mutu ba.
A halin yanzu, waɗanda ake zargin suna hannun ’yan sanda yayin da ake ci gaba da bincike domin gano nau’in sinadaran da ke cikin maganin da kuma musabbabin mutuwar mutanen.
