Wasu matasa sun yi wa Shugaban Ƙasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ihu tare da kirari na adawa da shi bayan kammala sallar Juma’a a babban masallacin Shehu Shagari da ke Abuja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Juma’a, 13 ga Nuwamba, 2026, jim kaɗan bayan shugaban ƙasar ya kammala sallah tare da barin harabar masallacin.
Wasu faifan bidiyo da suka yaɗu a kafafen sada zumunta sun nuna matasan na rera kirarin adawa da Tinubu yayin da ayarin motocinsa ke barin wurin.
Wani ganau da ya halarci sallar ya bayyana cewa matakin takaita zirga-zirgar jama’a da jami’an tsaro suka ɗauka saboda ziyarar shugaban ƙasar na daga cikin abubuwan da suka fusata masu ibada.
Majiyar ta ce Tinubu ya isa masallacin da misalin ƙarfe 1:49 na rana, inda jami’an tsaro suka hana wasu mutane shiga harabar masallacin, tare da toshe hanyoyin da suka kai wurin.
Ta ƙara da cewa an hana wasu masu ibada fita daga masallacin har sai shugaban ƙasar ya kammala tafiyarsa, lamarin da ya haifar da fushin wasu daga cikinsu.
Wasu daga cikin matasan sun riƙa rera kalaman “Ba ma yi, ba ma so” da kuma “Tinubu Must Go”, waɗanda ke nuna rashin goyon bayansu ga shugaban ƙasar.
Lamarin ya faru ne a daidai lokacin da ake ƙara samun hamayya ta siyasa gabanin zaɓen shugaban ƙasa mai zuwa.
A yayin sallar, babban limamin masallacin, Rabiu Suleiman, ya gabatar da wa’azi kan darussan da ke cikin Suratul Fatiha, inda ya yi kira ga Musulmi da su tabbatar da tauhidi tare da neman taimakon Allah.
Limamin ya kuma yi addu’ar samun zaman lafiya a Najeriya, da kuma Allah Ya ba shugaban ƙasar lafiya, hikima da ikon jagorantar Najeriya zuwa ga ci gaba.
Tinubu ya halarci sallar tare da mai ba shi shawara kan harkokin tsaro na ƙasa, Nuhu Ribadu; shugaban ma’aikatan fadar shugaban ƙasa, Femi Gbajabiamila; tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje; da kuma mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da Tinubu yake ɗan takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023, ya sha halartar sallar Juma’a a masallacin Area 1 da wasu masallatai a Abuja, ba tare da fuskantar irin wannan lamarin ba.
