Gwamnatin Tarayya ta ce za ta fara buga fasfo a Najeriya daga watan Mayun 2027, bayan kammala gina cibiyar samar da fasfo ta ƙasa a Abuja.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan yayin bikin aza harsashin ginin cibiyar da kuɗinta ya kai dala miliyan 70.
Ya ce cibiyar za ta fara da ƙarfin samar da fasfo miliyan shida a shekara, kafin daga bisani a ƙara ƙarfin zuwa miliyan 10.
Ministan ya bayyana cewa aikin, wanda ake gudanarwa tare da haɗin gwiwar kamfanin Iris Smart Technologies, zai rage dogaro da ƙasashen waje wajen samar da fasfo.
Ya kuma ce Najeriya za ta kasance ƙasa ta farko a Afirka ta Yamma da za ta mallaki cibiyar yin fasfo na zamani ta E-passport.
A nasa ɓangaren, Shugabar Hukumar Kula da Shige da Fice ta Ƙasa, Kemi Nana Nandap, ta ce cibiyar za ta magance matsalar ƙarancin fasfo da jinkirin samar da su da ’yan Najeriya suka daɗe suna fuskanta.
