Sunday, November 22, 2026
HomeLabaraiPeter Obi Ne Sahihin Dantakara Ta– Omo-Agege

Peter Obi Ne Sahihin Dantakara Ta– Omo-Agege

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Ovie Omo-Agege, ya sake jaddada goyon bayansa ga Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NDC, gabanin babban zaben 2027.

Omo-Agege ya bayyana hakan ne yayin da yake mayar da martani kan wani bidiyonsa da ya karade kafafen sada zumunta, inda yake bayyana goyon bayansa ga Shugaba Bola Tinubu.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar ta hannun mai ba shi shawara kan dabaru da sadarwa, Godwin Anaughe, tsohon sanatan ya ce bidiyon tsoho ne, kuma an dauke shi ne a watan Afrilun 2026, lokacin da yake cikin jam’iyyar All APC.

Ya ce ana yada bidiyon ne ba tare da bayyana sauye-sauyen siyasa da suka faru tun bayan daukar sa ba.

Omo-Agege ya zargi jam’iyyar APC ta Jihar Delta da wasu jami’an gwamnatin jihar da kokarin karkatar da matsayinsa na siyasa ta hanyar yada bidiyon da aka dauka kafin sauya shekarsa.

“Bidiyon gaskiya ne, amma an dauke shi ne watanni bakwai da suka gabata, kuma suna yada shi kamar an dauke shi ne a safiyar yau.

“Jam’iyyar da take da kwarin gwiwa kan ayyukanta ba ta bukatar mayar da tsohon bidiyo tamkar sabon labari. Sai dai wadda ke cikin matsanancin hali za ta yi hakan,” in ji sanarwar.

Tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce tun bayan komawarsa NDC a watan Mayun 2026, ya sha bayyana goyon bayansa ga takarar Obi, kuma bai sauya matsayinsa ba.

Ya kuma tabbatar da cewa har yanzu shi ne dan takarar sanatan NDC mai wakiltar Delta ta Tsakiya, yana mai cewa a yanzu biyayyarsa ta siyasa tana ga jam’iyyar adawa.

Omo-Agege ya ce matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta, musamman tsadar abinci da karancin ayyukan yi, su ne ya kamata APC ta mayar da hankali a kansu maimakon tsohon bidiyo.

“Abinci ya yi tsada, ayyukan yi sun yi karanci, fata ma ta yi karanci. Babu wani tsohon bidiyo da zai sauya wannan hali ko ya sanya abinci a kan teburin kowane gida,” in ji shi.

Ya kara da cewa ba zai bari tsofaffin al’amuran siyasa su dauke masa hankali ko su tsorata shi ba, yana mai cewa hankalinsa ya karkata ne kan babban zaben 2027.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments