Wednesday, November 25, 2026
HomeLabaraiKotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kísà Kan Zargin Kísà a...

Kotu Ta Yanke Wa Wani Mutum Hukuncin Kísà Kan Zargin Kísà a Kano

Wata Babbar Kotun Jihar Kano ta yanke wa wani mutum mai suna Isyaku Kabiru hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan ta same shi da laifin kashe Yahaya Dahiru ta hanyar daba masa sukudireba a ƙirji.

Mai shari’a Maryam Sabo ce ta yanke hukuncin, bayan Ma’aikatar Shari’a ta Jihar Kano ta gabatar da ƙara tare da samun nasarar tabbatar da laifin wanda ake tuhuma.

Sanarwar da Babban Mataimaki na Musamman ga Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a, Dakta Abubakar Tijjani Ibrahim, ya fitar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 19 ga watan Yulin 2015, a unguwar Darmanawa da ke cikin birnin Kano.

A cewar sanarwar, lauyan gwamnati mai gabatar da ƙara, Ummi Lawal Tudunwada, wadda ita ce mataimakiyar darakta a ma’aikatar, ta samu nasarar tabbatar da laifin ba tare da barin wata shakka ba.

Ta cimma hakan ne ta hanyar gabatar da shaidu biyu da kuma wasu muhimman kayayyakin shaida guda uku a gaban kotu.

Nigerian Post ta bibiyi cewa, Bayan nazarin shaidu da hujjojin da aka gabatar, kotun ta tabbatar da cewa Isyaku Kabiru ya aikata laifin kisan kai, inda ta yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Da yake tsokaci kan hukuncin, Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude, SAN, ya yabawa lauyan gwamnati bisa ƙwarewa da jajircewar da ta nuna wajen gudanar da shari’ar.

Ya kuma jaddada cewa ma’aikatar za ta ci gaba da tabbatar da cewa mutanen da suka aikata laifukan tashin hankali sun fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Sanarwar ta ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da ƙarfafa gurfanar da masu laifi a gaban kotu, domin tabbatar da cewa waɗanda aka zalunta da iyalansu sun samu adalci.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments