Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro na Ƙasa (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun samu gagarumar nasara ta hanyar cafke manyan shugabannin kungiyar ta’addanci ta Ansaru.
Ribaɗu ya bayyana wa ’yan jarida a Abuja cewa aikin ya gudana tsakanin watan Mayu zuwa Yuli, inda jami’an tsaro suka yi amfani da sahihan bayanan leken asiri wajen ƙaddamar da farmaki.
Ya ce wannan aiki ya rusa shugabancin ƙungiyar Ansaru mai alaƙa da Al-Qaeda, tare da bayyana shi a matsayin “mummunan rauni mafi girma da aka taɓa yi musu a tarihin ƙungiyar.”
Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa, NSA ya ƙara da cewa rundunar sojoji, hukumomin leƙen asiri da sauran jami’an tsaro ne suka aiwatar da wannan aiki na haɗin gwiwa, abin da ya nuna muhimmancin haɗa kai wajen yaƙi da ta’addanci a Najeriya.
Haka kuma, Ribaɗu ya buƙaci kafafen watsa labarai da su ci gaba da hana ’yan ta’adda samun damar amfani da kafafen jarida wajen yaɗa mugayen manufofinsu.