HomeSashen HausaDalilan Da Suka Sanya Shugaba Tinubu Ya Yanke Hutunsa Kafin Wa'adi- Rahoton...

Dalilan Da Suka Sanya Shugaba Tinubu Ya Yanke Hutunsa Kafin Wa’adi- Rahoton Daily Trust

-

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya dakatar da hutun da yake yi a ƙasashen waje, inda ya dawo Abuja ranar Talata domin ci gaba da gudanar da manyan ayyukan gwamnati.

Wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya bayyana cewa babban dalilin dawowar shugaban shine ƙarewar wa’adin dokar gaggawa a Jihar Rivers, wanda ya bukaci kulawarsa kai tsaye kan batutuwan tsaro da siyasa da suka taso a jihar.

Baya ga haka, rahoton ya ƙara da cewa shugaba Tinubu na bukatar gudanar shirye-shirye domin halartar babban taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 80 da zai gudana a birnin New York nan da makonni masu zuwa.

Ko da yake fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da cewa duk da cewa hutun nasa “na aiki” ne, inda yake ci gaba da kula da al’amuran gwamnati daga wajen ƙasa, akwai wasu batutuwan cikin gida da suka bukaci kasancewarsa a Abuja domin daukar matakai na kai tsaye.

Tuni dai masu goyon bayan gwamnati suka yaba da matakin shugaban, suna cewa hakan ya nuna jajircewarsa wajen fifita al’amuran ƙasa akan hutun kansa. Sai dai wasu ‘yan adawa sun yi nuni da cewa dawowar nan ta nuna irin gibin da ke akwai a wajen tsarin dake cikin gwamnatin, inda suka yi kira da a ƙarfafa tsarin gudanarwa wanda ba zai tsaya kan kasancewar shugaban kai tsaye ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Hukumar NSCDC A Katsina Ta Yi Sabon Shugaba

Hukumar Tsaro ta NSCDC reshen Jihar Katsina ta samu sabon kwamanda bayan sauyin shugabanci da ya gudana a ranar Litinin, 22 ga watan Satumba, 2025.   A...

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Horas Da Malamai 250 Da Faransifal 50, Don Inganta Ilmin Jihar

Ma’aikatar Ilimi a Matakin Farko da na Sakandire a jihar Katsina, haɗin gwiwa da Majalisar Turai (British Council), ta ƙaddamar da wani muhimmin shirin horaswa...

Most Popular