HomeSashen HausaGwamna Abba Ya Aika Sunayen Kwamishinoni Biyu Zuwa Majalisar Dokokin Kano

Gwamna Abba Ya Aika Sunayen Kwamishinoni Biyu Zuwa Majalisar Dokokin Kano

-

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya aika sunayen mutane biyu zuwa Majalisar Dokokin Kano domin tantancewa a matsayin sabbin Kwamishinoni kuma mambobin majalisar zartarwa ta jiha.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Asabar, gwamnan ya gabatar da sunayen Barrister Abdulkarim Kabir Maude daga Minjibir, wanda zai karɓi matsayin Babban Lauya na S (SAN) a gaban kotun koli gobe, da kuma Dr. Aliyu Isa Aliyu, Farfesa a fannin lissafi daga jami’ar North West U, Kano.

Barr. Maude, mai shekara 40, ya yi fice a harkar shari’a inda ya yi aiki fiye da shekara goma, kuma yana da digiri daga jami’o’i daban-daban ciki har da Jami’ar ABU Zaria da BUK.

Shi kuwa Dr. Aliyu, mai shekara 41, ya kware a fannin lissafi inda ya yi karantu a Najeriya da Jordan da Turkiyya, kuma yanzu haka shi ne Darakta Janar na Hukumar Ƙididdiga ta Jihar Kano.

A wani ɓangare, Gwamna Yusuf ya kuma amince da nadin Barrister Salisu Muhammad Tahir a matsayin sabon Babban Lauyan jiha (Solicitor-General) da Babban Sakataren na Ma’aikatar Shari’a ta Jiha.

Gwamnan ya ce shigar da sabbin mambobin majalisar zartarwa na daga cikin matakan da gwamnatinsa ke ɗauka domin tabbatar da cancanta da kwarewa da gaskiya a aikin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular