Wata Mata Ta Yi Garkuwa Da Kanta, Tare Da Neman Kuɗin Fansa Daga Mijinta A Edo
Rundunar ƴansandan Jihar Edo ta kama wata mata mai suna Chioma Success mai shekaru 27, wadda ake zargi da yin ƙaryar an yi garkuwa da ita domin ta karɓi kudin fansa a wajen mijinta.
An kuma kama wasu mutane biyu da ake zargin ta haɗa baki da su da suka haɗa da Martins Chidozie Mai shekaru 23 da Osita Godfrey Mai shekaru 33.
Mai magana da yawun rundunar, ASP Eno Ikoedem, ta bayyana cewa an kama waɗanda ake zargi bayan bincike da aka gudanar kan rahoton garkuwa da matar.
Ta ce a ranar 27 ga Oktoba, 2025, wani mutum mai suna Paul Adaniken ya kai rahoto ofishin ƴansanda na New Etete, inda ya bayyana cewa ya bar matarsa, Chioma Success Ezebie, da ɗansu mai shekara uku, Andrea Ojiezelabor, a gida kafin ya tafi kasuwancinsa.
Daga baya, sai aka kira shi a waya da wata bakuwar lamba, inda aka shaida masa cewa an sace matarsa da ɗansa.
Mai magana da yawun ta ce masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya su naira miliyan biyar (₦5,000,000) a matsayin kudin fansa kafin su sake su.
Ta ƙara da cewa yayin da bincike ke gudana, an gano cewa ɗan uwanta, Osita Godfrey, wanda a farko ake ganin yana taimaka wa ‘yan sanda da bayani, shi ma yana da hannu a cikin lamarin, kuma hakan ya sa aka kama shi.
Bayanan da ya bayar bayan kama shi ne suka kai ga cafke Chioma Success, wadda ta amsa cewa ta haɗa baki da mutanen domin ƙirƙirar labarin yin garkuwa da ita, da nufin karɓar kuɗi daga mijinta.
