Daya daga cikin makusantar tsohuwar Jarumar Kanywood Hadiza Gabon, ya tabbatar wa Jaridar ALFIJIR NEWS, wanda a yanzu jarumar ta fara tinanin dauke zauren Shirin daga Kaduna zuwa Kano.
“Hakan na biyo wa ne duba da irin cin fuskan da Masoya Adam A Zango Suka fara yi mata, ɗaya daga cikin Ma’aikatan ta a zauren Shirin Aliyu Mai Nasara yace an fara neman wuri a Kano domin komawa can da ci gaba da Shirin.”
“Hakan ya kara buɗe wani sabon fai-fai ne, na yadda Masoya fitaccen jarumin Kanywood din Adam A Zango Suke bayyana ita tsohuwar jarumar Hadiza Gabon da yin butulci ga Adamu, abin Mamaki har yanzu dai Adamu bai ce komai ba akan lamarin.
Daga Barr Nuraddeen Isma’eel
