HomeSashen HausaAmurka Da Najeriya Na Dab da Cimma Yarjejeniyar Tsarin Tsaro Don Yakar...

Amurka Da Najeriya Na Dab da Cimma Yarjejeniyar Tsarin Tsaro Don Yakar Boko Haram da ISIS

-

Danmajalisar wakilan Amurka, Riley Moore, ya ce Amurka da Najeriya na dab da cimma matsaya kan wani tsarin tsaro na dabaru da nufin yaƙar Boko Haram da ISIS a Najeriya.

 

Moore, wanda ya kai ziyara Najeriya tare da wasu ’yan majalisar Amurka, ya bayyana cewa sun yi tattaunawa masu kyau da gwamnatin Najeriya kan batutuwan tsaro.

 

Ya ce ziyarar ta ba shi damar ganawa da wasu daga cikin waɗanda ta’addanci ya shafa, inda ya ce abin da ya gani ya girgiza zuciya.

 

Dan majalisar ya kuma ce zai miƙa rahoto ga Shugaban Amurka, Donald Trump, domin bayyana hanyoyin da za a bi wajen haɗa kai da gwamnatin Najeriya don kawo ƙarshen kashe-kashen da ake dangantawa da ta’addanci.

 

A yayin ziyarar, tawagar ta gana da Mai Ba da Shawara kan Tsaron Kasa, Nuhu Ribadu, a Abuja, tare da ziyartar wasu al’ummomi a arewacin Najeriya.

 

Moore na daga cikin ’yan siyasar Amurka da ke ikirarin ana tsananta wa Kiristoci a Najeriya, kuma a ranar 7 ga Nuwamba ya gabatar da kuduri a majalisar wakilan Amurka kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Nijeriya Ta Musanta Zargin Leken Asiri Kan Jirginta Da Ke Burkina-Faso

Rundunar Sojin Sama ta Najeriya (NAF) ta karyata jita-jitar da ke cewa jirginta kirar C-130 da ya sauka ba tare da shiri ba a Bobo-Dioulasso,...

Duniya Za Ta Fuskanci Ƙalubale, Idan Najeriya Ta Wargaje– Inji Sanata Kashim Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.   Kamar yadda...

Most Popular