Mataimakin Shugaban Ƙasa a Najeriya, Kashim Shettima ya ce gwamnatin Tinubu ba za ta taɓa bari Najeriya ta ruguje a hannunta ba, komai rintsi.
Kamar yadda Nigerian Post ta samu daga Aminiya, Shettima ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a wajen yaye ɗaliban Cibiyar Nazarin Manufofi da Muhimman Buƙatu ta Ƙasa (NIPSS) da ke Kuru a Jihar Filato.
Ya ƙara da cewa idan har Najeriya ta tarwatse to ’yan ƙasar, sama da mutum miliyan 50 za su fantsama su tsallaka Turai.
Don haka ya ce zai fi zama alheri ga duniya idan Najeriya ta ɗore a matsayin ƙasa guda.
