HomeSashen HausaZa a Gudanar Da Cikakken Bincike Kan Shugaban NMDPRA– Inji ICPC

Za a Gudanar Da Cikakken Bincike Kan Shugaban NMDPRA– Inji ICPC

-

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Su (ICPC) ta tabbatar da karɓar ƙorafi daga attajirin ɗan kasuwa, Alhaji Aliko Dangote, kan Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur ta Kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed.

 

A ranar Lahadi, Dangote ya zargi Ahmed da kashe dala miliyan biyar ($5m) a matsayin kuɗin karatun ’ya’yansa a makarantu da ke ƙasar Switzerland.

 

Attajirin ya kuma zargi shugaban NMDPRA da yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa, tare da miƙa ƙorafi ga ICPC bisa zargin cin hanci da rashawa.

 

Da take martani ga ƙorafin, ICPC a ranar Talata ta ce za ta binciki lamarin.

 

“ Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka Masu Alaka da Su (ICPC) na sanar da cewa ta karɓi ƙorafi a hukumance a yau Talata, 16 ga Disamba, 2025, daga Alhaji Aliko Dangote ta hannun lauyansa. Ƙorafin ya shafi Shugaban NMDPRA, Alhaji Farouk Ahmed.

 

“ICPC na so ta bayyana cewa za a binciki ƙorafin yadda ya kamata,” in ji sanarwar da kakakin ICPC, John Odey, ya fitar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

‎Lokacin Gwamnatin Babana, Sabi’u Tunde Ya Yi Ƙarfin Da Ministoci Tsoron sa Suke– Inji Fatima Buhari

Fatima Buhari, ‘yar fari ga marigayi Muhammadu Buhari, ta ce Tunde Sabiu, tsohon sakataren shugaban ƙasa, yana da babban tasiri a lokacin mulkin mahaifinta ta...

‎Gwamnan Kano Ya Yabawa Tinubu da Abba Bichi Kan Aikin Titin Wuju-Wuju a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana matukar godiyarsa ga Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu bisa amincewar da ya bayar na sa hannun Gwamnatin...

Most Popular