HomeSashen Hausa‎Gwamnatin Benue Ta Umarci Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa Masu Son Tsayawa...

‎Gwamnatin Benue Ta Umarci Masu Riƙe Da Muƙaman Siyasa Masu Son Tsayawa Takara Da Su Yi Murabus

-

‎Gwamnatin Jihar Benue ta umurci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a mukaman zabe na shekarar 2027 da su yi murabus daga mukaman da suke rike da su nan take.

‎Kamar yadda ne Nigerian Post ta samu daga Daily Nigerian, wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan wata 16 ga Disamba, 2025, wadda Mataimakin Gwamnan Jihar Benue, Mista Sam Ode, ya sanya wa hannu, kuma aka fitar da ita ga manema labarai a ranar Laraba a Makurdi.

‎A cewar sanarwar, an dauki matakin ne sakamakon karuwar harkokin siyasa a jihar a baya-bayan nan.

‎Sanarwar ta ce: “Duba da karuwar harkokin siyasa a jihar a baya-bayan nan, tare da lura da irin sha’awar da mutane ke nunawa wajen neman mukaman shugabanci domin inganta nagartaccen shugabanci da kuma ci gaba da kyawawan nasarorin da gwamnatin Rev. Fr. Hyacinth Iormen Alia ta cimma.

‎“Saboda haka, ana rokon masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a mukaman zabe da su bayyana niyyarsu tare da mika takardar murabus dinsu yadda ya dace,” in ji wani bangare na sanarwar.

‎Sanarwar ta kuma bukaci wadanda abin ya shafa da su mika dukkan takardun neman tsayawa takara ko bayyana sha’awa ga ofishin Mataimakin Gwamnan Jihar Benue kafin ranar Alhamis, 18 ga Disamba, 2025, domin duba su da kuma daukar matakan da suka dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Kwamishinan ’Yansanda Ya Karɓi Baƙuncin Sabon Kwamandan Rundunar Sojin Saman Najeriya Da Aka Turo Katsina

Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, MNIM, ya karɓi bakuncin sabon Kwamandan da aka turo na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, 213...

Tsohon gwamnan Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa, ya koma jam’iyar APC

Bafarawa da magoya bayansa sun bayyana komawa jam'iyar APC a babban xakin taro na gidansa dake jihar Sakkwato a ranar Laraba.   Tsohon Gwamnan ya ce magoya...

Most Popular