HomeSashen HausaGamayyar jam'iyyun adawa a Najeriya na shirin rajistar sabuwar jam'iyyar ADA don...

Gamayyar jam’iyyun adawa a Najeriya na shirin rajistar sabuwar jam’iyyar ADA don kifar da APC a zaɓen 2027

-

Jagororin jam’iyyun hamayya na Najeriya a ƙarƙashin inuwar ƙungiyar hadaƙa ta Nigeria National Coalition Group (NNCG) na neman rajistar All Democratic Alliance (ADA) domin ta zama sabuwar jam’iyyar da za su yi amfani da ita domin fafatawa da jam’iyyar APC a zaɓe mai zuwa.

Nigerian Post ta samu cewa, tuni NNCG ta miƙa takardar neman rajistar jam’iyya ga Hukumar INEC a hukumance, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Wasiƙar wadda suka aika zuwa ga shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu a ranar 19 ga watan Yuni, shugaban ADA na ƙasa Cif Akin Ricketts da sakataren riƙo Abdullahi Musa Elayo ne suka sanya mata hannu, sannan INEC ta karɓa tare a ranar 20 ga Yunin.

A wasiƙar, sun rubuta cewa, “muna neman INEC ta amince da buƙatarmu ta yi wa ƙungiyarmu ta All Democratic Alliance ta zama jam’iyyar siyasa.”

Taken jam’iyyar dai shi ne ‘Adalci ga kowa’ sannan masara ce tambarinta.

Daga cikin na gaba-gaba wajen yunƙurin samar da haɗaka da za ta fuskanci jam’iyyar APC mai mulki akwai tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar da tsohon gwamnan jihar Ribas Rotimi Amaechi da tsohon gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai da tsohon shugaban majalisar dattawar ƙasar, Sanata David Mark da Umar Arɗo da sauransu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

PDP Ta Yi Tur Da Kamen Da Aka Yi Ma Tsohon Gwamna Aminu Waziri Tambuwal

Jam’iyyar PDP a jihar Sokoto ta yi Allah-wadai da kamawa tare da tsare tsohon gwamnan jihar, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, tana zargin jam’iyyar APC da...

DA ƊUMI-ƊUMINSA: Ana Ci Gaba Da Gangamin Bikin Ranar Matasa Ta Duniya A Sassan Najeriya

Matasa a lungu da saƙo na sassan ƙasar Najeriya, suna ci gaba da gangamin bikin tunawa da ranar Matasa ta Duniya, inda su ke ci...

Most Popular