Gwamnatin kasar Saudiyya ta amince da binne fitaccen dan kasuwar nan na Najeriya, Aminu Dantata a birnin Madina mai alfarma.
Babban sakatare mai zaman kansa, Mustapha Junaid, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
A cewarsa, za a dauki gawar mamacin ne daga Abu Dahabi ta ƙasar Dubai zuwa ƙasar Saudiyya.
Ana sa ran za a yi jana’izar ne a safiyar ranar Litinin a birnin Madina.
Alhaji Aminu Dantata, na É—aya daga cikin hamshakan attajiran Najeriya, ya rasu a Dubai bayan ya yi fama da doguwar jinya ya rasu yana da shekaru 94 a Duniya.