HomeSashen HausaGwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar...

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

-

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda yake jagorantar wata babbar tawaga domin halartar jana’izar fitaccen attajiri kuma dattijon kasa, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a birnin Madina mai alfarma, da ke Kasar Saudiyya.

Marigayin ya rasu da safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa.

Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar.

Tawagar tana dauke da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, tsohon gwamnan Jigawa Barr. Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun dattawan jihar.

Da ya ke jawabi kafin tafiya daga filin jirgin sama, Gwamna Yusuf ya bayyana marigayi Dantata a matsayin “uba ga mutane da dama, wanda kyautatawarsa da kishinsa ga dan Adam suka wuce kima da iyaka.”

Gwamnan ya jaddada cewa halartar tawagar Kano a jana’izar da za a gudanar a Madina na nuni da irin girmamawa da godiya da al’ummar Kano ke da ita ga marigayin da irin gudummawar da ya bayar a rayuwarsa.

Ana sa ran jana’izar za ta ja hankalin wakilan jihohi da na gwamnatin tarayya, ‘yan uwa da abokan arziki, masana addini da masoya daga sassa daban-daban na duniya, dukkansu domin yin addu’a da neman gafara ga marigayin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Jirgin Rano Air Ya Samu Matsalar Injin Saman Iska Kan Hanyar Sa Ta Zuwa Katsina

Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NCAA) ta bayar da umarnin tsayar da wani jirgin sama na kamfanin Rano Air mai lamba 5N-BZY,...

Nasarori 12 Da Dakta Abdullahi Umar Ganduje Ya Kafa A Shugabancin APC

Jerin basarori 12 da Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya kafa a shugabancin jam'iyyar APC na ƙasa da babu shugabanta da ya taɓa kafawa a cikin...

Most Popular