HomeSashen HausaTinubu ya tura Shettima a ɓoye don ya ziyarci Buhari a Asibitin...

Tinubu ya tura Shettima a ɓoye don ya ziyarci Buhari a Asibitin London

-

Shugaba Bola Tinubu ya tura mataimakinsa, Kashim Shettima, domin ya ziyarci tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a wani asibiti da ke London a ranar Litinin, kamar yadda wasu majiyoyi masu tushe su ka shaida wa jaridar TheCable.

Tsohon shugaban ya dade yana fama da rashin lafiya, kamar yadda Empowered Newswire ta fara rawaito wa, amma ana ganin yana samun sauƙi a halin yanzu.

Shettima ya kasance a Addis Ababa, Habasha, a gayyatar Firayim Minista Abiy Ahmed Ali domin halartar ƙaddamar da shirin Green Legacy Initiative (GLI) na ƙasar ta Gabashin Afirka.

Stanley Nkwocha, mai magana da yawun Shettima, shi ne ya tabbatar da cewa, shugabansa ya kai ziyara London amma ya ce ba zai iya cewa komai game da manufar ziyarar ba domin bai san cikakken jadawalin tafiyar ba.

Sai dai Tinubu wanda ke wata ziyara ta ƙasa a St Lucia, ya umurci Shettima da ya tafi London domin duba tsohon shugaban ƙasar.

TheCable ta fahimci cewa, Shugaba Tinubu ya umarci Shettima da ya binciki yanayin lafiyar Buhari tare da tabbatar da an ba shi kulawa ta musamman har zuwa samun lafiya.

Shettima wanda ya tashi daga Addis Ababa a daren Lahadi, inda ya isa London ranar Litinin kafin ya tafi wani Asibiti da ba a bayyana sunansa ba domin isar da saƙon Tinubu ga Buhari, in ji majiyoyin.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular