Matashin ɗangwagwarmayar Comrade Haidar Hasheem ya ce, wa su tsirarun mutane masu ƙazamin nufi suke yada wani labari mara tushe a kafafen sada zumunta da ke cewa Muhammad Babangida, ɗan tsohon shugaban kasa Ibrahim Badamasi Babangida (IBB), ya ƙi amincewa da nadin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya masa na chairman BOA.
Nigerian Post ta samu cewa, ya ce sun tabbatar da cewa labarin ƙarya ne tsagwaronta, domin ba Muhammad Babangida bane ya fitar da sanarwar da ke yawo ba. Lambar da ke jikin takardar da aka yaɗa da kuma sa hannun da ke cikinta duk ba nasa ba ne.
A cewar Comrade Haidar Hasheem Kano, wani makirci ne da ɓatanci da ƙoƙarin jefa shakku a tsakanin shugaban ƙasa da manyan ‘yan Najeriya, musamman waɗanda ke da sunaye da martaba a cikin al’umma.
Ya ce, Muhammad Babangida bai fito ya musanta nadin ba, kuma babu wata cikakkiyar shaida daga gare shi ko daga hannunsa da ke nuna ya ƙi karɓar kujerar. Wannan yana nuni da cewa an ƙirƙiri wannan labari ne domin yaudarar jama’a da haddasa ruɗani.
Daga karshe, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi hattara da labaran ƙarya da ake yawan yaɗawa, su nemi gaskiya daga ingantattun majiyoyi kafin yarda da kowace irin sanarwa.