HomeSashen HausaBa Gaskiya Ba Ne Maganar Da Ƙungiyar Likitoci Ta Ƙasa-da-ƙasa Tayi Na...

Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Ƙungiyar Likitoci Ta Ƙasa-da-ƙasa Tayi Na Cewar Sama Da Yara 650 Sun Mutu Sakamakon Yunwa A Katsina- inji Hon. Sahalu Shargalle

-

Mai taimaka ma Gwamna kan harakokin siyasa a shiyyar Daura, Hon. Sahalu Shargalle ya ce, Jihar Katsina ba cima-zaune Bace ‘yankine da ya shahara da Noma da Kiwo, ya bayyana haka a wani martanin da ya rubuta kan rahoton Kungiyar likitoci ta Duniya MSF da ta yi ma jihar Katsina.

Dr. Sahalu Umar Shargalle, PhD dake a (NDA,KADUNA), a cewar sa, babu wata hujja dake nuna cewa Yara a jihar Katsina na fuskantar ƙarancin Abinci mai gina jiki domin kuwa yanki ne da ya shahara da Noma da Kiwo- da saura sana’o’in dogaro da kai.

Kamar yadda Nigerian Post ta bibiyi rahoton, Mai taimaka ma Gwamna kan harakokin siyasa a shiyyar Daura, Hon. Sahalu Shargalle, ya yi nuni da cewa, jihar Katsina nada ƙasar Noma kimanin 2.4 Milayan hektas(Murabba’i), wanda ana Noma kimanin Hektas 1.6 Million, inda kimanin Hektas 800,000 Ake samar da masana’antu aciki.
“Don haka, ba gaskiya ba ne maganar da ƙungiyar Likitoci ta kasa-da kasa tayi nacewar sama da Yara 650 sun mutu dalilin yunwa a katsina” inji Sahalu Umar Shargalle.

Sai dai ya ƙara da cewa, ko mutanen da ake gani ‘yan kasashen waje ne dake maƙobtaka da jihar Katsina ke zauwa yawon barace -barace da sana’o’in Kaskanci domin Neman Abinci wanda su ne ke zuwa wajan waɗannan Mutanen domin(Medicine Sans frontier, MSF) Daniyyar Neman Maganin Kwamaso.

Dr. Sahalu Umar Shargalle ya yi zargin cewa ire-iren waɗannan ƙungiyoyin suna fakewa ne da bayar da tallafi don wawure albarkatun kasashen Afirika da sauran kasashe masu tasowa, “Muna sane da irin cuta da wawure albarkatun kasashen da wadannan kungiyoyi sukeyi dasunan tallafi wanda a hakikanin gaskiya ba haka lamarin yake ba, Za su zo da kalaman barazana da tsoratarwa da dora munanan kalamai irin su; Yunwa, Talauci, Rashin tsaro, Rashin Ilimi, Rashin dai-daito tsakanin Maza da mata, Addini, Cututtuka, da dai Sauran su, musamman ga Kasashe ko Jahohin dasuka fahimci suna da Arziki ko Ma’adanai domin suzo suyita kwasa da zummar taimakawa, ko dauki” kamar yadda Sahalu Umar Shargalle ya jaddada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

INTERNAL SECURITY: Katsina Police Foil Kidnap Attempts, Rescue 28 Victims

Katsina State The Katsina State Police Command has successfully foiled two separate kidnap attempts in Sabuwa Local Government Area, rescuing a total of 28 victims...

APC National Legal Adviser Vows to Unite Party Members

The newly appointed National Legal Adviser of the All Progressives Congress (APC), Barrister Murtala Aliyu Kankia, has pledged to prioritize the unity of party members...

Most Popular