Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, tare da taimakon iyalai da mambobin tawagar gudanarwa, ya lakabawa jami’an ‘yan sanda dari biyar da tamanin da tara (589) lambar karin girma amatsayin jinjina bisa sadaukarwar da suka nuna wajen hidima ga Hukumar ‘Yan Sanda ta Najeriya.
Jami’ai uku (3) daga cika anyi masu karin girma da sabbin mukaman Assistant Commissioner of Police (ACP), yayin da sauran aka ɗaga su daga mukamin Sergeant zuwa Inspector, da kuma daga Corporal zuwa Sergeant.
Nigerian Post ta bibiyi rahoton cewa, bikin dai ya kasance wani muhimmin mataki a rayuwar aikin jami’an da aka ƙara wa matsayi, inda manyan jami’an ‘yan sanda, abokai, iyalai, da masu fatan alheri suka halarci bikin.
A jawabin sa, CP Bello Shehu ya nuna godiya ga Sufeton Janar na ‘Yan Sanda, IGP Kayode Adeolu Egbetokun, da Hukumar Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) bisa ganin jami’an sun cancanci karin matsayi, tare da umartar su da su ninka ƙoƙarinsu wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata.
ACP Abdullahi Muhammad Dattijo, wanda ya yi jawabi a madadin waɗanda suka samu karin girman ya gode wa IGP da PSC bisa wannan karramawa, tare da gode wa CP Bello Shehu bisa jagoranci da goyon bayan da yake bayarwa.
Daga nan ya yi alkawarin ci gaba da daga tutar Hukumar ‘Yan Sanda ta Najeriya, Ya kuma gode wa duk wandanda suka halarci bikin