Wata kotun tarayya a ƙasar Kanada ta haifar da cece-kuce bayan da ta danganta manyan jam’iyyun siyasa na Najeriya, Peoples Democratic Party (PDP) da All Progressives Congress (APC), da abubuwan da ta bayyana a matsayin ayyuka masu kama da ta’addanci.
Hukuncin ya samo asali ne daga shari’ar wani ɗan Najeriya mai neman mafaka, Douglas Egharevba, wanda kotun ta ƙi buƙatarsa bisa kasancewarsa tsohon memba na PDP da APC.
PDP ta yi watsi da hukuncin tana mai cewa babu tushe kuma an yi shi ne da son zuciya. Ita kuwa APC ta ce kotun ba ta da ikon ayyana jam’iyya a matsayin ƙungiyar ta’addanci, tana mai jaddada cewa jam’iyyarta ta dimokuradiyya ce.
Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta bayyana hukuncin a matsayin abin da zai iya haifar da illa ga dangantakar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Kanada, yayin da masana suka yi gargadin cewa wannan lamari na iya kawo kalubale ga tsarin dimokuradiyya a Afirka.