HomeSashen HausaKotun Tarayya Ta Yanke Wa Jagoran Ansaru Hukuncin Shekaru 15 a Gidan...

Kotun Tarayya Ta Yanke Wa Jagoran Ansaru Hukuncin Shekaru 15 a Gidan Gyaran Hali

-

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ma wani jagoran ƙungiyar ta’addanci ta Ansaru, mai suna Mahmud Muhammad Usman (wanda aka fi sani da Abu Bara’a/Abbas/Mukhtar), hukuncin shekaru 15 a gidan gyaran hali bayan ya amsa laifinsa kan tuhumar haƙar ma’adinai ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun nuna cewa Usman ya amsa laifin hakar ma’adinai ba tare da izini ba, inda kuɗaɗen da ake samu daga wannan aiki ake zargin yana amfani da su wajen saya makamai domin gudanar da ayyukan ta’addanci.

Abu Bara a da wani ɗan kungiyar, Abubakar Abba (wanda aka fi sani da Isah Adam/Mahmud Al-Nigeri), an gurfanar da su ne bisa zarge-zargen laifuka 32 da suka haɗa da ta’addanci, samar da kudi don ta’addanci da kuma amfani da makamai. Duk da haka, Abba ya ƙi amsa dukkanin tuhumar da ake masa, kuma shari’ar tasa za a ci gaba da saurran ta.

Kotun ta ba da umarnin cewa waɗanda ake tuhuma su ci gaba da zama a hannun Hukumar Tsaro ta Jiha (DSS) yayin da ake cigaba da shari’ar. An dai ɗage sauraron shari’ar sauran tuhume-tuhumen har zuwa 21 ga watan Oktoba, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

SAKON ƘARSHEN SHEKARA NA KATSINA TIMES: Mun Fuskanci Barazana Da Kalubale A Shekarar 2025– Inji Malam Muhammad Danjuma Katsina

Tunda farko, ya yi godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki, tare da salati da aminci ga Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW), iyalansa (AS) da sahabbansa (RA),...

Obi Na Shirin Shiga ADC Yayin Da Jam’iyyar Za Ta Yi Babban Taron Ta Na Ƙasa a 2026

Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na Labour Party (LP), Peter Obi, na dab da shiga jam’iyyar ADC, gabanin babban zaɓen shekarar 2027. Wata majiya a jam’iyyar...

Most Popular