Ma’aikatar Shari’a ta jihar Katsina ta naɗa Basira Umar a matsayin mace ta farko da za ta rike mukamin Babbar Magatakarda ta Babbar Kotun Katsina tun bayan kafa jihar a 1987.
A rahoton Daily Nigerian, wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Musa Usman, Daraktan Hulda da Jama’a na Babbar Kotun jihar, ya fitar ga manema labarai a Katsina a ranar Asabar.
A cewarsa, wannan naɗin ya biyo bayan ritayar Malam Mustapha Hassan-Rumah daga aikin gwamnati.
Ya bayyana cewa Babban Magatakarda shi ne babban jami’in kula da dukiyar kotu, wanda ke da alhakin tsarawa da gudanar da kasafin kuɗi da sauran harkokin kuɗi.
“Haka kuma Babban Magatakarda shi ne shugaban gudanarwa na ma’aikatar shari’a, wanda ke jagorantar harkokin yau da kullum.