HomeSashen HausaGwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zamansu A Kurkuku

Gwamnatin Tarayya Za Ta Tallafa Wa Fursunoni Bayan Kammala Zamansu A Kurkuku

-

Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa tana aiki tare da Ƙungiyar Lauyoyi ta Nijeriya (NBA) domin ƙirƙirar shirye-shiryen tallafawa fursunoni bayan sun kammala zaman kurkuku da kuma bayar da taimakon shari’a kyauta ga waɗanda ke jiran gurfanarwa.

Ministan Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis bayan ziyarar bazata da ya kai Gidan Gyaran Hali da ke Kuje a Abuja.

Ya ce wannan ziyara da ya kai tare da Shugaban ƙungiyar lauyoyi (NBA), Afam Josiah Osigwe (SAN), na da nufin duba halin da ake ciki a gidan gyaran halin da kuma gano hanyoyin inganta tsarin gyaran halin da yin adalci.

Tunji-Ojo ya bayyana cewa haɗin gwuiwar da ke tsakanin ma’aikatarsa da NBA na cikin shirin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na “Renewed Hope”, wanda ke son inganta tsarin gyaran hali da rage cunkoson gidajen yari. Ya ƙara da cewa wannan shiri zai taimaka wajen shirya fursunoni su koma cikin al’umma cikin sauƙi tare da rage yiwuwar sake aikata laifi.

Ya ƙara da cewa ma’aikatar cikin gida za ta ci gaba da jagoranci ta hanyar aikatawa, inda ya jaddada muhimmancin ƙirƙirar hanyoyin da za su inganta walwalar fursunoni da jami’ar gidan yari. “Ta wannan hanyar, za mu rage cunkoso a gidajen gyaran hali da kuma taimaka wa fursunoni su koma cikin al’umma cikin nasara,” in ji shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano

Ɓarawo Ya Sace Motar Ayarin Mataimakin Gwamna A Gidan Gwamnatin Kano Wani barawon mota ya kutsa cikin Gidan Gwamnatin Kano da sanyin safiyar Litinin ya kuma...

‎Yansanda Sun Kama Masu Aikata Laifuka Daban-daban, Sun Ceto Mutane 47 da Aka Yi Garkuwa da Su a Jihar Katsina

Rundunar ‘Yansanda ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ta samu nasarori masu yawa a yakin da take yaki da laifuka, ciki har da kama mutanen...

Most Popular