HomeSashen HausaBudurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren...

Budurwa Ta Hallaka Kanta A Jihar Borno Bayan Tilasta Ma Ta Auren Dole

-

Wata matashiya ta kashe kanta a karamar hukumar Gubio ta jihar Borno, bayan mahaifinta ya tilasta mata aure da ɗaya daga cikin abokansa.

 

Shafin jaridar Zagazola Makama ya rawaito cewa lamarin ya faru ne da yammacin jiya Lahadi da misalin ƙarfe 6:20, inda majiyoyi suka bayyana cewa marigayiyar ta sha matsin lamba daga iyayenta don ta amince da auren da aka shirya mata, duk da cewa tana ƙaunar wani daban.

 

Wani mai sa ido kan kare haƙƙin yara a yankin, Bukar Fantami Gubio, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa damuwa da matsin lambar da ta fuskanta ne suka sa ta ɗauki ranta.

 

Ya yi kira ga hukumomin kare haƙƙin ɗan adam da jami’an tsaro da su gudanar da bincike tare da ɗaukar matakin hana irin wannan auren dole a nan gaba.

 

Rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar Borno ba su fitar da wata sanarwa ta hukuma kan lamarin ba har zuwa lokacin da ake kammala wannan rahoto.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

An Fara Binciken Tsohon Gwamna Daga Kudanci Kan Zargin Kitsa Juyin Mulki A Najeriya

Rahotanni sun bayyana cewa ana binciken wani tsohon gwamna daga ɗaya daga cikin jihohin kudancin Najeriya bisa zargin alaƙa da wasu jami’an soji 16 da...

Budurwa Ta Hallaka Kanta Saboda Saurayinta Ya Yi Ma Ta Kishiya A Jihar Enugu 

Wata budurwa mai shekaru 22, mai suna Odama Mary Agado, ta kashe kanta bayan ta gano saurayinta tare da wata mace a jihar Enugu.   VANGUARD ta...

Most Popular