Rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta gurfanar da Malam Iliyasu Mohammed Gamawa, tsohon alƙali a jihar, a gaban Kotun Majistare ta Ɗaya da ke fadar gwamnati, bisa zargin yanke hukunci a kotu duk da cewa ya riga ya yi ritaya daga aikin gwamnati.
A cewar Hukumar Kula da Harkokin Shari’a ta Jihar Bauchi, Gamawa ya ajiye aikinsa ne bayan cikar wa’adinsa, kuma hukumar ta amince da ritayarsa. Sai dai duk da haka, a ranar 18 ga Fabrairu 2025, mako guda bayan ya yi ritaya, an zarge shi da yanke hukunci a wata shari’a da ta shafi Alhaji Adamu Dama da S. I. Dama a kotun Dewu.
Bayan samun koke daga hukumar Shari’a ƙarƙashin jagorancin sakatare Dr. Ibrahim Danjuma, rundunar ‘yan sanda ta gudanar da bincike, daga bisani ta gurfanar da shi a kotu.
An tuhumi tsohon alƙalin da laifin sojan-gona da kuma saɓa dokokin aikin gwamnati, laifuka da su ka saba wa sashi na 179 na Dokokin Jihar Bauchi.
A zaman kotu, Gamawa ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, inda alkalin ya yanke masa hukuncin daurin shekaru biyu, ko kuma biyan tarar naira dubu ɗari ɗaya (₦100,000).
Da yake magana da manema labarai, sakataren hukumar Shari’a ta jihar Bauchi, Dr. Ibrahim Danjuma, ya yi gargadi ga duk masu kokarin yi wa hukumar zagon ƙasa, yana mai jaddada cewa hukumar ba za ta yi sassauci ba ga duk wanda ya aikata irin wannan laifi. Ya ce hukuncin zai zama izina ga masu niyyar take ka’idojin aikin shari’a.
