Sojojin Rundunar 8 Division ta Najeriya a Sokoto sun samu gagarumar nasarar kawar da fitaccen shugaban ’yan bindiga, Kachalla Kallamu, a yankin Sabon Birni, Jihar Sokoto.
An kashe Kallamu ne a wani samame na musamman da sojoji suka gudanar tare da hadin gwiwar ’yan sa-kai a yankin Kurawa, da safiyar Litinin.
Kallamu, wanda babban na hannun daman shugaban ’yan bindiga Bello Turji ne, ya kasance daya daga cikin wadanda suka addabi al’ummar Sabon Birni da hare-hare, garkuwa da mutane da kuma tada tarzoma a yankin.
Rahotonni sun bayyana cewa an kashe shi ne tare da daya daga cikin manyan masu samar wa Turji da kayan aiki da bayanan sirri, a wani artabu da ya faru da safiyar litinin.
Rahotanni sun ce Kallamu, wanda asalinsa daga Garin-Idi a Sabon Birni, ya dawo ne cikin yankin bayan tserewa wani farmaki da sojoji suka kai masa a watan Yunin 2025, inda ake zargin ya shige Kogi domin buya.
