Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta (EFCC) ta ce ba ta da alaka da siyasa a yadda take gudanar da ayyukanta.
Hukumar ta bayyana hakan ne yayin da take mayar da martani ga zargin da tsohon Antoni Janar na Tarayya, Abubakar Malami, ya yi cewa an soke belinsa ne saboda halartar wani taron siyasa a Jihar Kebbi.
