Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, MNIM, ya karɓi bakuncin sabon Kwamandan da aka turo na Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, 213 Forward Operating Base Katsina, a ziyarar girmamawa da ya kai masa a yau Laraba, 17 ga Disamba, 2025. Ziyarar ta kasance ne domin ƙarfafa haɗin gwiwa da fahimtar juna tsakanin hukumomin tsaro.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, Kwamandan 213 FOB Katsina, Air Commodore C. E. Illoh, ya nuna godiyarsa bisa kyakkyawar tarba da aka yi masa a yayin ziyarar. Ya bayyana cewa ziyarar ta zo ne domin sanin shugabancin rundunar ’yan sanda a jihar tare da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar da ake da ita tun farko.
Ya kuma nemi ƙarin goyon baya da haɗin kai domin cimma burin samar da Jihar Katsina mai aminci da tsaro.
A nasa jawabin, Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Katsina, CP Bello Shehu, MNIM, ya yaba wa Kwamandan bisa ganin dacewar kai masa ziyara a ofishinsa. Ya amince da rawar da Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ke takawa wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci da laifuka, tare da jaddada aniyarsa ta ƙarfafa kyakkyawar alaƙar aiki tsakanin hukumomin.
Bayanin hakan na kunshe acikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar, DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar.
