Wani ɗan asalin jihar Katsina, Ahmed Idris Zakari, ya sami ƙarin girma a Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), inda aka naɗa shi zuwa mukamin Assistant Commander General of NDLEA, wani mukami dake daf da na ƙarshe a tsarin shugabancin hukumar.
Ahmed Idris Zakari, wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Katsina, ya samu wannan matsayi ne sakamakon jajircewarsa, kwarewa da kuma gudummawar da ya bayar tsawon shekarun da ya shafe yana aiki a hukumar, musamman a fannin yaƙi da miyagun ƙwayoyi da kare lafiyar al’umma.
Masu ruwa da tsaki da dama sun bayyana wannan cigaba a matsayin abin alfahari ga jihar Katsina dama Arewa gaba ɗaya, inda suka yaba da yadda ƴayan jihar ke cigaba da samun manyan mukamai a hukumomin ƙasa.
An yi addu’ar Allah Ya sanya alheri a wannan ƙarin girma, Ya kuma ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin adalci da gaskiya, tare da cigaba da bada gudummawa wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi a Najeriya.
