Kungiyar Afenifere, wadda ke wakiltar al’ummar Yarbawa a fannin siyasa da zamantakewa, ta bayyana goyon bayanta ga hare-haren jiragen yakin Amurka da aka kai kan sansanonin kungiyar ta’addanci ta ISIS a jihar Sokoto.
Kungiyar ta yaba wa gwamnatin tarayya bisa abin da ta bayyana a matsayin hare-haren da suka kasance masu muhimmanci kuma a kan lokaci, duba da halin rashin tsaro da ke kara ta’azzara a sassan kasar nan.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ta tabbatar da cewa an gudanar da harin ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Amurka, domin kai wa sansanonin ‘yan ta’addan ISIS da ke jihar Sokoto.
