HomeSashen HausaHarin Da Amurka Ta Kai 'Yan ta'adda Ne Kaɗai Ya Shafa– Inji...

Harin Da Amurka Ta Kai ‘Yan ta’adda Ne Kaɗai Ya Shafa– Inji Gwamnatin Sokoto

-

Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da cewa harin sama na haɗin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka ya kai hari kan sansanonin ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Tangaza, ba tare da asarar rayukan fararen hula ba.

 

Sanarwar da Darakta-Janar na yaɗa labarai na fadar gwamnati, Abubakar Bawa, ya fitar ta ce harin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin raunana ’yan ta’adda da ’yan bindiga a jihar da kan iyakokin arewa maso yammacin Najeriya.

 

Gwamnatin ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan wasu abubuwa masu shakku da aka gano kusa da garin Jabo a Ƙaramar Hukumar Tambuwal, tare da jaddada cewa babu fararen hula da suka rasa rayukansu.

 

Jihar Sokoto ta yi maraba da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, tana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci da laifukan kan iyaka.

 

Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai da addu’o’i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Afenifere Ta Goyi Bayan Harin Da Amurka Ta Kai a Sokoto

Kungiyar Afenifere, wadda ke wakiltar al’ummar Yarbawa a fannin siyasa da zamantakewa, ta bayyana goyon bayanta ga hare-haren jiragen yakin Amurka da aka kai kan...

‎Majalisar Wakilai Ta Umarci A Yi Gyare-gyare a Kundin Sabbin Dokokin Haraji Bayan Samun Kura-kurai

Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin sake duba sabbin dokokin gyaran haraji da aka amince da su kwanan nan, biyo bayan zargin bambance-bambance tsakanin dokokin...

Most Popular