Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya amince da bai wa ’ya’yan ’yan Majalisar Jiha biyu da suka rasu, damar tsayawa takara, domin neman cike guraben kujerun iyayensu a Majalisar Dokokin Jihar ta Kano.
Matakin wanda ya shafi kujerun wakilcin Ungogo da Birnin Kano, inda ’ya’yan kowane daya daga cikin ’yan majalisar za su fafata a zaben cike gurbin kujerun karkashin tutar jam’iyyar NNPP.
Majiyoyi daga cikin jam’iyyar sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin kokarin NNPP na tabbatar da ci gaba da wakilci da kuma girmama gudunmawar da ’yan majalisar suka bayar wajen hidimar al’ummar yankunansu a lokacin da suke raye.
Ana sa ran wannan mataki zai jawo ra’ayoyi mabanbanta a fagen siyasar Jihar Kano, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen tunkarar zabukan cike gurbin kujerun da ke tafe.
