Kotun ɗaukaka ƙara ta tabbatar da hukuncin kisa da aka yanke wa Abdulmalik Tanko, wanda aka samu da laifin garkuwa da kuma kashe Hanifa, yarinya ƴar shekara takwas, Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan duba ƙarar da aka shigar, inda ta ce hujjojin da aka gabatar sun isa su tabbatar da laifukan da aka tuhumi wanda ake ƙara.
Mai shari’a A.R. Muhammad, wanda ya jagoranci zaman kotun, ya bayyana cewa hukuncin da kotun ƙasa ta yanke ya yi dai dai da tanadin doka, kuma babu wani kuskure a shari’ar da zai sa a soke ko a rage hukuncin, Ya ƙara da cewa an bi dukkan matakan shari’a yadda ya kamata tun daga matakin bincike har zuwa yanke hukunci.
Kotun ta kuma ja hankalin gwamnati da ta gaggauta aiwatar da hukuncin kisa, domin tabbatar da adalci ga iyalan wadda abin ya shafa, hana aikata laifuka makamantan haka a nan gaba, da kuma kare al’umma daga miyagun laifuka.
Hukuncin ya jawo martani daga al’umma, inda da dama ke ganin cewa matakin da kotu ta ɗauka zai zama darasi ga masu aikata laifukan garkuwa da kashe kashe, musamman waɗanda ke shafar yara.
