HomeSashen Hausa‎Dalilan Da Suka Sa Aka Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf...

‎Dalilan Da Suka Sa Aka Ɗage Sauya Sheƙar Gwamna Abba Kabir Yusuf Zuwa APC

-

Wasu bayanai sun fito kan dalilin da ya sa aka ɗage shirin sauya sheƙar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, daga jam’iyyarsa zuwa jam’iyyar APC mai mulki, duk da an riga an kammala shirye-shiryen farko.

‎A ranar Juma’a, jaridar DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa gwamnan ya kammala tanadin sanar da sauya sheƙarsa a Ranar Litinin mai zuwa. Sai dai kafin aiwatar da shirin, aka samu sauyin jadawali Wanda ya haifar da ɗagewar matakin.

‎Rahotanni sun nuna cewa hedkwatar APC ta ƙasa ta riga ta shirya Gwamnan zai kasance mutum na farko da za a yi wa rajista a Kano a sabon tsarin rajistar jam’iyyar na yanar gizo. Bisa wannan tsari, tsohon Gwamnan Kano kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ne zai raka Gwamna Abba Yusuf zuwa mazabarsa ta Diso Ward domin yin rajista a manhajar jam’iyyar tare da karɓar katin membobinsa.

‎Bayan kammala rajistar gwamnan, shi ma Gwamna Abba Yusuf zai raka Ganduje zuwa Garinsa na Dawakin Tofa Domin sabunta rajistarsa a sabon tsarin jam’iyyar.

‎Sai dai duk da waɗannan shirye-shirye, Wasu dalilai na ciki sun sanya aka ɗage aiwatar da sauya sheƙar, lamarin da ya haifar da jinkiri a sanarwar da ake sa ran yi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

Katsina Police Received 29 New ASPs From The Nigeria Police Academy, Wudil

The Katsina State Police Command has received 29 newly posted Assistant Superintendents of Police (ASPs) from the Nigeria Police Academy, Wudil. Welcoming the officers, the...

Yawancin Fulanin Da Suke Ta’addanci Ba Su Da Addini, Ba Su San Allah Ba– Nasir El Rufa’i ‎

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i, ya bayyana cewa yawancin mutanen Fulani da ake zargi da aikata ta'addanci da kashe kashe a sassa daban...

Most Popular