Thursday, July 16, 2026
HomeLabaraiBa Za Mu Yi Shiru Kan Matsalolin Da Ke Addabar Al'ummar Katsina...

Ba Za Mu Yi Shiru Kan Matsalolin Da Ke Addabar Al’ummar Katsina Ba- Dr. Kurfi

Dr. Bashir Kurfi ya ce ba zai daina bayyana ra’ayinsa kan matsalolin da ke addabar al’umma ba, yana mai cewa abin da ya faru da shi ya ƙara tabbatar masa da cewa akwai buƙatar dattawa su ci gaba da magana kan batutuwan da suka shafi rayuwar jama’a.

A wata hira da kafar yaɗa labarai ta JBC Hausa ta yi da, Dr. Kurfi, ya ce yana tare da talakawa, kuma a shirye yake ya ci gaba da fafutukar ganin an samu sauƙi ga al’umma.

“Ba abin da zai girgiza mu a duniya. Muna tare da talakawanmu da al’ummarmu, idan al’umma na cikin bala’i, dole mu yi magana domin a samu sassauci a rayuwa. Ba wanda zai maida mu bayi.”

Ya ce shi ɗan asalin Jihar Katsina ne mai shekaru sama da 70, kuma ya shafe kusan shekaru 40 yana koyarwa a makaranta, yana mai cewa tsare shi ya sa ya ƙara ganin wajabcin dattawa su ci gaba da faɗar gaskiyar abin da suke gani.

Dr. Kurfi ya kuma yi nuni da matsalolin tsaro da suka addabi wasu sassan Jihar Katsina, yana cewa hakan na shafar harkokin noma musamman a lokacin damina.

“Yanzu damina ake, amma ba ko’ina ake iya noma ba saboda matsalar tsaro. Idan ba mu yi magana kan waɗannan matsaloli ba domin a nemo mafita, ta yaya za a samu gyara?”

Ya ƙara da cewa, ba zai yi shiru ba kan batutuwan da suka shafi yunwa, ilimi da tsaron rayuwar al’umma.

A kwanakin baya dai, an gurfanar da Dr. Kurfi, a gaban kotu kan wasu zarge-zarge da ya musanta, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce daga ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam da sauran masu ruwa da tsaki.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments