Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Gwamnatin Tarayya, Abubakar Malami (SAN), ya zargi Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) da daukar matakan hana shi cikakken ’yancinsa na shari’a da kare kansa yadda doka ta tanada.
A cikin wata sanarwa da Mai Taimaka Masa kan Harkokin Yaɗa Labarai, Mohammed Bello Doka, ya sanya wa hannu, Malami ya ce DSS na ci gaba da hana lauyoyinsa damar ganinsa, lamarin da ya hana shi tuntuba, ba da umarni, da kuma shirya takardun shari’a yadda ya dace.
Malami ya bayyana hakan a matsayin tauye hakkokin ɗan Adam, yana mai cewa irin waɗannan matakai sun sabawa tanade-tanaden kundin tsarin mulkin Najeriya.
“Abin da ke faruwa ya nuna wani salo da ake fara kama mutum kafin bincike, sannan a fara neman hujjoji bayan tsare shi, wanda hakan ya saɓa doka da kuma ’yancin da kundin tsarin mulki ya tanada,” in ji sanarwar.
Ya ƙara da cewa abin damuwa ne matuƙa ganin yadda DSS ke aiwatar da abin da ya kira tsarewa, sannan neman hujjoji daga baya, yana mai jaddada cewa hakan barazana ce ga bin doka da oda ta ƙasa.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, DSS ba ta fitar da wata sanarwar martani kan zargin da tsohon Ministan ya yi ba.
