Fitacciyar jaruma a masana’antar Kannywood da Nollywood, Rahama Sadau, ta shirya bikin ɗaga darajar fina-finan Arewacin Najeriya.
Jarumar ta ce ta shirya bikin ne domin tallata fina-finan Arewacin Nijeriya domin ɗaga martabar fina-finan da zummar samun karɓuwa a ƙetare.
Rahama Sadau ta bayyana hakan ne a yayin jawabin da ta gabatar a wajen bikin fina-finan da aka gudanar a dandalin Murtala Square da ke Jihar Kaduna.
Manyan jaruman Kannywood da suka yi fice, ciki har da Ali Jiya, Umar M. Shareef, Abdul D One da sauran fitattun ’yan fim, sun halarci taron waɗanda suka fito domin nuna goyon baya ga jarumar.
