HomeLabaraiHisba Ta Bayyana Wuraren Da Ta Haramta Ƙwallon Ƙafa Lokacin Ramadan a...

Hisba Ta Bayyana Wuraren Da Ta Haramta Ƙwallon Ƙafa Lokacin Ramadan a Katsina

-

Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta bayyana cewa ba ta haramta wasan ƙwallo gaba ɗaya a watan Ramadan ba, sai dai ta ɗauki matakin hana yin wasan da daddare a kan tituna da kuma wuraren da ke haddasa cunkoso da kawo cikas ga zirga-zirga.

‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da Jami’in Sashen Fasahar Sadarwa na Hisbah a Dandume, Malam Bin Haris, ya fitar domin fayyace matsayar hukumar ga al’umma.

‎A cewar sanarwar, an takaita wasan ƙwallo da daddare ne musamman a wuraren da ke kawo tangarda ga zirga-zirgar ababen hawa, da kuma a lokutan da jama’a ke tafiya masallatai domin gudanar da ibadu a watan Ramadan. Hukumar ta ce matakin na da nufin kare lafiyar al’umma, tabbatar da tsaro, da samar da kwanciyar hankali a wannan wata mai alfarma.

‎Haka kuma, hukumar ta yi kira ga al’umma da su guji yaɗa jita-jita ko karkatar da bayani dangane da umarninta, tare da bin doka, mutunta hanyoyi, da kuma bada haɗin kai ga jami’an tsaro domin samun zaman lafiya da nutsuwa a duk tsawon watan Ramadan.

‎Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta jaddada cewa ƙoƙarinta na ci gaba da kasancewa ne wajen gyara al’umma da kare martabar addini ba tare da tauye hakkokin jama’a ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

FG Denies ADC Use of Eagle Square for Abuja Convention

The African Democratic Congress (ADC) has said it was denied access to both Eagle Square and the Moshood Abiola National Stadium for its planned national...

Albaba Announces Return Bid for Katsina Assembly Seat

Hon. Aliyu Albaba has declared his intention to contest for a seat in the Katsina State House of Assembly to represent Katsina Local Government Area...

Most Popular