Kwamandan runduna ta 3 ta sojojin Najeriya, kuma kwamandan Operation Enduring Peace (OPEP), Manjo Janar Maxwell Dangana, ya baiwa wani soja mai suna Private Utim Terwase kyautar kuɗi har Naira dubu 500 saboda ƙin karɓar cin hancin da wani da ake zargi da garkuwa da mutane ya yi masa.
NIGERIAN POST ta bibiyi cewa, Rahotanni sun bayyana cewa sojan ya kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke ƙoƙarin tserewa, sai mutumin ya yi masa tayin N500,000 domin ya sake shi, amma sojan ya ƙi karɓar kuɗin, sannan ya miƙa shi ga hukumomi.
Kakakin Operation Enduring Peace, Kyaftin Polycarp Chinonso Oteh, ya tabbatar da hakan, inda ya ce an miƙa kyautar a madadin babban kwamandan rundunar ta hannun Kwamandan Sector 6, Kanal Philimon Malgwi.
Ya ce Manjo Janar Dangana ya yaba wa sojan bisa gaskiya, ladabi da ƙwarewar aiki da ya nuna.
Kwamandan ya bayyana cewa wannan hali ya nuna jajircewa da biyayya ga aikin soja, inda ya fifita aikinsa da kishin ƙasa a kan son abin duniya.
Ya ƙara da cewa an ba sojan kyautar N500,000 ne domin girmama amincinsa da kuma jajircewarsa wajen gudanar da aikinsa, wanda ya yi daidai da adadin kuɗin cin hancin da ya ƙi karɓa.
