Majalisar Koli ta Shari’a ta Najeriya (SCSN) ta gargaɗi ’yan siyasa da magoya bayansu da su guji duk wani abu da ka iya haddasa tashin hankali gabanin zaɓen 2027, tana mai cewa babu wata kujera ko burin siyasa da ya kai a zubar da jinin ’yan Najeriya.
A cikin wata sanarwa da babban sakatarenta, Farfesa Ahmad Bello Dogarawa, ya fitar ranar Laraba, majalisar ta bukaci ’yan siyasa su guji kalaman tunzura jama’a, siyasar addini da ƙabila, barazana da amfani da ’yan daba.
Ta kuma buƙaci ’yan Najeriya su mallaki katin zaɓensu (PVC), su tabbatar da bayanan rajistarsu tare da fitowa ranar zaɓe domin zaɓar shugabannin da suke so.
Majalisar ta yi kira ga jami’an tsaro da su gudanar da ayyukansu cikin adalci, tare da kare masu kaɗa ƙuri’a da jami’an zaɓe, yayin da ta yi Allah wadai da sayen ƙuri’u, satar akwatin zaɓe da hana mutane kaɗa ƙuri’a.
Haka kuma, ta shawarci jam’iyyu da magoya bayansu su amince da sahihin sakamakon zaɓe ko kuma su bi hanyoyin doka wajen ƙalubalantar sakamakon.
Ta jaddada cewa nasarar zaɓe da mulki na ɗan lokaci ne, amma shugabanci amana ce da ke buƙatar gaskiya da riƙon amana.
