Gwamnatin Jihar Sokoto ta tabbatar da cewa harin sama na haɗin gwiwar sojojin Najeriya da Amurka ya kai hari kan sansanonin ’yan ta’adda a ƙaramar hukumar Tangaza, ba tare da asarar rayukan fararen hula ba.
Sanarwar da Darakta-Janar na yaɗa labarai na fadar gwamnati, Abubakar Bawa, ya fitar ta ce harin na daga cikin matakan da ake ɗauka domin raunana ’yan ta’adda da ’yan bindiga a jihar da kan iyakokin arewa maso yammacin Najeriya.
Gwamnatin ta kuma bayyana cewa ana ci gaba da bincike kan wasu abubuwa masu shakku da aka gano kusa da garin Jabo a Ƙaramar Hukumar Tambuwal, tare da jaddada cewa babu fararen hula da suka rasa rayukansu.
Jihar Sokoto ta yi maraba da haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka, tana mai cewa hakan na da muhimmanci wajen yaki da ta’addanci da laifukan kan iyaka.
Gwamnatin ta kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai da addu’o’i domin samun zaman lafiya mai ɗorewa.
