Tuesday, June 30, 2026
HomeLabaraiMatsalolin Tsaro Za Su Zama Tarihi A Shekarar 2026– Shugaba Tinubu

Matsalolin Tsaro Za Su Zama Tarihi A Shekarar 2026– Shugaba Tinubu

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen Duniya a shekarar 2026, domin murƙushe dukkan barazanar tsaro da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da cikakken ikon ƙasar Najeriya.

‎Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin saƙon sabuwar shekarar 2026 da ya gabatar ga ’yan Najeriya, inda ya jaddada cewa ba za a samu ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ba sai an tabbatar da tsaro da zaman lafiya.

 

‎Tinubu ya ce, Najeriya na fuskantar barazanar ’yan ta’adda da ’yan fashi, amma gwamnati na ɗaukar matakai masu ƙarfi, ciki har da hare-haren haɗin gwiwa da abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, musamman Amurka, domin raunana ƙungiyoyin ta’addanci.

‎“A ranar 24 ga watan Disamba, an kai hare-hare masu ƙarfi kan sansanonin ’yan ta’adda a wasu sassan Arewa maso Yamma,” inji shugaban.

 

Nigerian Post ta bibiyi cewa, ‎Tunibu ya jaddada cewa, rundunonin tsaro za su ƙarfafa musayar bayanai da daidaita ayyuka da ƙasashen waje a 2026, tare da tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ’yan ƙasa.

Haka kuma, ‎game lda tsarin tsaro, Tinubu ya nuna goyon bayansa ga ’yan sanda na jihohi, tare da tanadin tsarin doka da kula da masu tsaron dazuka.

‎A ɓangaren tattalin arziki, shugaban ya ce 2026 za ta zama shekarar bunƙasar tattalin arziki, inda za a hanzarta shirin Renewed Hope Ward Development Programme da nufin samar da ayyukan yi ga ’yan Najeriya miliyan 10.

‎Ya kuma tabbatar da ci gaba da manyan ayyukan more rayuwa, tare da kira ga ’yan Najeriya da su bada gudummawar su wajen gina ƙasa.

‎A ƙarshe, Tinubu ya yi wa ’yan Najeriya fatan sabuwar shekara mai cike da zaman lafiya, tsaro da ci gaba.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments