HomeLabaraiMusulman Najeriya 89,000 Ne Suka Yi Umrah a 2025– Inji Saudiyya

Musulman Najeriya 89,000 Ne Suka Yi Umrah a 2025– Inji Saudiyya

-

Hukumomin ƙasar Saudiyya sun bayyana cewa kusan Musulman Najeriya 89,000 ne suka gudanar da aikin ibadar Umrah a shekarar 2025, inda kashi 92 cikin 100 suka shigo da bizar Umrah.

 

Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya, Dakta Tawfiq Al-Rabiah, ne ya bayyana hakan a wani muhimmin taro da aka gudanar a Abuja tsakanin hukumomin Najeriya da tawagar Saudiyya.

 

Ya ce jirage kusan 420 ne suka tashi daga Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah domin tallafa wa ayyukan Umrah na ‘yan Najeriya.

 

Al-Rabiah ya jaddada ƙudirin Saudiyya na ƙarfafa haɗin gwiwa da Najeriya domin tabbatar da tsaro, sauƙin tafiya da ingantacciyar hidima ga mahajjatan Najeriya. Ya kuma bayyana shirye-shiryen Masarautar na yin aiki tare da Najeriya wajen shirin Hajjin 1447 Hijira, yana mai cewa “Insha Allah Hajjin 2026 zai zama mafi alheri.”

 

A nasa bangaren, Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi, ya bayyana ziyarar a matsayin muhimmin mataki a dangantakar Najeriya da Saudiyya, yana mai yabawa Masarautar kan ci gaba da inganta walwalar mahajjata da ayyukan Hajji da Umrah.

 

Ministan Harkokin Waje, Yusuf Maitama Tuggar, ya ce ziyarar ta zama tarihi, kasancewar ita ce karo na farko da Ministan Hajji da Umrah na Saudiyya ke zuwa Najeriya, yana mai jaddada ƙudirin ƙasashen biyu na ƙarfafa haɗin gwiwa a harkokin Hajji da Umrah.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

CAF Strips Senegal of AFCON 2025 Title, Awards It to Morocco

The Confederation of African Football (CAF) has stripped Senegal of the 2025 Africa Cup of Nations (AFCON) title and awarded it to Morocco. In a statement...

Mutane 23 Sun Mutu, Sama da 100 Sun Jikkata a Harin Bama-bamai a Maiduguri

‎Aƙalla mutane 23 sun mutu, yayin da mutane 108 suka jikkata sakamakon wasu jerin fashewar bama-bamai da suka auku a daren Litinin. ‎ ‎Rundunar ’yan sandan Jihar...

Most Popular