Friday, June 26, 2026
HomeLabaraiSojojin Saman Najeriya Sun Hallaka 'Yanbindiga 27 a Katsina

Sojojin Saman Najeriya Sun Hallaka ‘Yanbindiga 27 a Katsina

Rundunar sojojin sama ta Najeriya (NAF), a karkashin rundunar FANSAN YANMA, ta samu babban nasara a jihar Katsina bayan kai farmaki na sama da ya hallaka wasu ‘yan bindiga a ƙaramar hukumar Faskari

 

Zagazola ya samu labarin cewa an gudanar da farmakin ne a safiyar 1 ga watan Fabrairu, inda aka kai hari kan sansanonin da ake zargin ‘yan bindiga suna taruwa a dajin Shawu–Mununu Ruwan Godiya a yankin faskari.

 

Majiyoyi sun ce farmakin ya biyo bayan dogon bincike na sama da ya tabbatar da kasancewar ‘yanbindiga masu makamai a yankin Bakori–Guga, waɗanda ake zargi da kai hare-hare kwanan nan.

 

An yi kira ga al’umma da su ci gaba da bayar da sahihan bayanai ga hukumomi domin taimaka musu wajen gano motsin ‘yan ta’adda.

RELATED ARTICLES

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Most Popular

Recent Comments