HomeLabaraiIdan Tinubu Bai Janye Maganar Haraji Ba Zai Gani A Akwatin Zaɓensa–...

Idan Tinubu Bai Janye Maganar Haraji Ba Zai Gani A Akwatin Zaɓensa– Sheikh Yakubu Musa Katsina

-

Sheikh Yakubu Musa Katsina ya bayyana takaicin sa akan irin yadda musamman ‘yan arewa suka kasa cim amfanin gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

A cewar shehin malamin shugaba Bola Tinubu ya cuce su musamman yadda baya sauraran koken ‘yan arewa a cikin sha’anin mulkin sa kamar yadda yake sauraren ‘yan kuɗi

A wani rahoto da Popular News ta wallafa, Sheikh Yakubu Musa ya ce yana magana ne a madadin kungiyar izala tunda kowa ya san matsayin sa a cikin ta.

Waɗanda kalaman dai suna zuwa ne a daidai lokacin da shehin malamin ke gudanar da karatun tafsirin Alqur’ani na watan azumi.

Ya kuma cigaba da bayanin cewa idan har shugaban ƙasa bai canza kudurin sa ba na ƙakabawa talakawa haraji ba, lallai zai gani a kwaryar zaɓen shi.

Sheikh Yakubu Musa ya ce Allah ya yi wa Nijeriya arziki amma gwamnati ta yi amfani da shi akan ‘yan ƙasa maimakon haka sai ta bijiro da batun haraji ga talakawa

Ya ce akwai takaici kwarai da gaske irin yadda shugaban ƙasa ke bin talakawa da ke neman abincin da za su ci, ana karbar haraji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

LATEST POSTS

CAF President Calls for Unity After AFCON 2025 Final Controversy

The President of the Confederation of African Football (CAF), Patrice Motsepe, has called for unity and integrity in African football following the controversy that trailed...

ADC Activities Suspended in Katsina by Court Order

A High Court in Katsina State has ordered the suspension of all activities of the African Democratic Congress (ADC) across the state, pending the hearing...

Most Popular